Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Sauke Shugaban Hukumar PPPRA

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayyar karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ya sauke shugabannin hukumomin dake kula da harkokin hada-hadar man fetur na DPR da PPPRA da PEF a Najeriya.

Wannan, kamar yadda muka samu na zuwa ne biyo bayan soke hukumomin uku a ɓangaren mai kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta PIB, ta tanada.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shugaban kasar ya sawa sabuwar dokar hannu a watan Agusta da ya gabata.

An kafa wasu sabbin hukumomi biyu da za su maye gurbinsu, wato Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority da Nigerian Upstream Regulatory Commission, kuma hukumomin biyu za su sa ido ne kan hakar mai da sarrafa shi a Najeriya.

Ƙaramin ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva ya tabbatar da kafa sabbin hukumomin da fara aikinsu kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ƙaddamar da hukumar darektocin sabbin hukumomin a Abuja ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta kare ayyukan ma’aikatan tsoffin hukumomin uku da aka soke duk da cewa an sallami shugabanninsu daga mukamansu.

Labarai Makamanta