Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Dira Birnin Ikko

Rahotanni daga fadar Shugaban ƙasa birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya domin ƙaddamar da wasu ayyuka a yau.

Rahotanni na cewa cikin ayyukan da zai ƙaddamar har da wasu sabbin jiragen ruwa na yaƙi a tashar ruwa ta sojin ruwan ƙasar da ke Victoria Island.

Tuni hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas LASTMA ta ba jama’a shawara da su kiyayi bi ta titin Ahmadu Bello sakamakon ziyarar shugaban.

Tuni sojoji da ƴan sanda da jami’an DSS suka cika unguwar Victoria Island wanda nan ne shugaban zai je.

Ana kuma sa ran bayan ƙaddamar da ayyukan zai halarci ƙaddamar da wani littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.

Labarai Makamanta