Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi Da Mutum Biyu A Jíhar Kaduna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu mazauna jihar biyu sun rasa rayukansu sakamakon tashin bam da aka dasa ta karkashin kasa a karamar hukumar Chikun da ke jihar.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00 na ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba bayan motar mutanen ta bi ta kan bam din da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka binne shi a wani wuri da ake kira Zangon Tofa a yankin Kabrasha. dake karamar hukumar Chikum.

Mazauna kauyen na jigilar amfanin gona da aka girbe ne lokacin da lamarin ya afku. Da yake tabbatar da lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana sunayen mutanen da suka rasu a matsayin Babajo Alhaji Tanimu da Safiyanu Ibrahim.

Ya kuma ce Gwamna Nasir El-Rufai ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su. El-Rufai wanda ya yi addu’a kan Allah ya ji kan mamatan, ya roki mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, kafin ɗaukar mataki daga gwamnati.

Labarai Makamanta