Da Dumi-Dumi: Ba A Ga Wata Ba Za A Yi Azumi 30 Ne – Fadar Sarkin Musulmi

“Ba mu samu rahotan ganin Wata ba a Nijeriya, don haka a cika Azumi talatin a yi Sallah ranar Lahad” Cewar Fadar Sarkin Musulmi.

Wata majiya daga fadar Sarkin Musulmin ta sanar da cewa, a dukkanin yankunan da akace an ga wata, babu wani Hakimi ko shugaba daga yankin da ya kira fadar Sarkin Musulmin ya tabbatar da cewa an ga wata.

Daular Musulunci ta Saudiyya ita ma ta bada sanarwar cewa ba a ga wata ba a kasar, saboda haka za a cika azumi talatin ne a tashi da Sallah ranar Lahadi.

Muna Addu’a da fatan Allah amshi ibadunmu da muka gabatar Allahumma Amin.

Related posts