Da Dumi-Dumi: Ayu Ya Zama Sabon Shugaban PDP

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Iyorchia Ayu, ya zama sabon Shugaban uwar jam’iyyar PDP.

Ayu, wanda bai samu wanda yayi takara da shi ba zai jagoranci jam’iyyar da sauran shugabanni 20 da aka zaba.

Nasarar tashi ta biyo bayan babban taro ne da jam’iyyar ta PDP ta gudanar a jiya a babban birnin tarayya Abuja.

Rikicin cikin gida na cigaba da ci wa jam’iyyar tuwo a kwarya, wanda masana ke ganin na iya haifar wa jam’iyyar tarnaki a kokarinta na ganin ta dare Madafun Iko a shekarar 2023.

Labarai Makamanta