Da Dumi-Dumi: An Yi Tankade A Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa fitaccen ɗan jarida, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya daga Jigawa, Sani Zorro, hadimin uwargidan sa Aisha Buhari.

Sani Zorro zai yi aiki a ofishin uwargidan shugaban kasa a matsayin babban mai taimaka mata kan harkokin hulɗa da jama’a da tsare-tsare.

Bayan haka, a cikin sanarwar wanda Garba Shehu ya fidda ranar Asabar, shugaba Buhari ya amince da a sauya wa wasu manyan hadimai da ke aiki a ofishin uwargida Aisha wuraren aiki. An umarce su da su garzaya ofishin sakataren gwamnatin tarayya don sanin inda suka dosa.

Waɗanda sauyin ya shafa sun haɗa da Mohammed Abdulrahman, babban likitan matar shugaban kasa, sai kuma Hadi Uba da Wole Aboderin.

Sai dai kuma hadimar uwargida Aisha dake kula da harkokin yau da kullum da shirya bukukuwa, Zainab Kazeem ce kaɗai wanda garambawal ya wancakalar.

Labarai Makamanta