Da Dumi-Dumi: An Yi Nasarar Kashe Dogo Gide

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar an yi nasarar hallaka shahararren ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Dogo Gide a wani gumurzu a dajin Kuyanbana.

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna. A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa Gide ya mutu ne a ranar Lahadi bayan mataimakin kungiyarsa na yan Bindiga, Sani Dan Makama ya bindige shi kamar yadda ya yi wa Buharin Daji.

Tsohon shugaban ‘yan bindigan ya dade yana adabar garuruwa a jihohin Zamfara, Niger, Kaduna, Katsina da Kebbi tsawon shekaru.

Majiyar ta ce: “Mataimakin Dogo Gide wanda ake kira Sani Dan Makama ne ya kashe shi bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a dajin Kuyambana da ya hada Zamfara – Birnin Gwari da Dogon Dawa.”

Labarai Makamanta