Da Dumi-Dumi: An Sake Dawo Da Dokar Korona A Saudiyya

Rahotanni dake shigo mana daga Ƙasar Saudiyya na bayyana cewar an sake dawo da dokar tilasta bayar da tazara da saka takunkumi a Masallacin Ka’aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina, kamar yadda hukumomin da ke kula da Masallatan Biyu Masu Daraja na Saudiyya suka bayyana.

Matakin zai fara aiki ne daga ranar Alhamis, inda hukumomin suka ce yanzu saka takunkumi da bayar da tazara ya zama wajibi.

Hukumomin sun ce matakin ya shafi masu aikin Umrah da masu ɗawafi da sauran masu Ibada a masallatan biyu.

Sannan an yi gargaɗi ga baƙi da ma’aikatan Masallatan biyu su mutunta dokar.

Dokokin za su rika aiki a cikin gidaje da kuma waje inda mutane ke mu’amalar yau da kullum.

A ‘yan kwanakin nan masu kamuwa da korona na karuwa a Saudiyya.

Labarai Makamanta