Da Dumi-Dumi: An Kulle Masallatai Da Makarantar Abduljabbar Bisa Umarnin Kotu

Gwamnatin Jihar Kano ta bi umarnin kotu, inda ta garƙame masallatan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma makarantarsa.

Haka-zalika, bisa bin umarnin kotun, gwamnatin ta kuma kwace littattafan sa guda 189, inda ta kai su zuwa ɗakin kararu.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a ranar 15 ga watan Disamba, Babbar Kotun Shari’a ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Hukuncin ya zo ne biyo bayan kama Abduljabbar da laifin furta kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a wasu karaturrukan sa.

Laifin ya saɓa da sashe na 382 da 375 na kundin shari’ar Kano na 2000.

Da ya ke yanke hukuncin, Sarki Yola ya kuma umarci gwamnatin Kano da ta rufe dukka masallatai da makarantar Abduljabbar, sannan ta kwace littattafan sa 189 da ya kafa hujja da su lokacin shari’ar.

Tuni dai gwamnatin ta cika wannan umarni, inda ta garƙame masallacin nasa na Filin Mushe a Gwale da Jamiurrasul da ke sharada.

An ga kuma jami’an tsaro na shawagi a guraren masallatan da makarantar, inda tuni a ka aike da littattafan na sa zuwa ɗakin karatu na jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply