Da Dumi-Dumi: An Hallaka Kwamandan ISWAP Abu Sufyan A Tafkin Chadi

Gamayyar harin sama da sojojin Nijeriya su ka kai ya hallaka wani babban kwamandan ISWAP, Abu Sufyan da mayaƙan sa da dama a yankin Tafkin Chadi a Jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta jiyo cewa Rundunar Sojin Sama, NAF, a wani ɓangare na ‘Operation Hadin Kai’ ce ta kai hare-hare a kan gurin ajiye makaman ISWAP ɗin da ke Kusuma da Sigir a ƙaramar hukumar Marte a Borno, a ranar Lahadi.

Rundunar ta kai harin ne bayan ta samu bayanan sirri cewa akwai ƴan ta’addan a yankin, inda su ke haɗuwa domin su kai hare-hare a yankin da sojoji su ka mamaye.

Wata majiyar sirri ta shaidawa PRNigeria cewa an kai harin ne ta sama ta amfani da jiragen yaƙin gwamnati, inda a ka kai mummunan hari kan kayan yaƙin ƴan ta’addan.

“Bayan nan kuma sauran ƴan ta’addan da su ke tserewa a ka tare su a ka hallaka su suma,” in ji majiyar.

Labarai Makamanta