Da Dumi-Dumi: An Daga Darajar Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Yola Zuwa Asibitin Jami’a

Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana jira daga ƙarshe shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya dake Yola wato FMC Yola da ta zama asibitn koyarwa na Jami ar Modibbo Adama dake Yola.

Darakta yada labarai na ofishin Sakataren gwamnatin tarayya Mr Willie Bassey ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Amincewar dai ta biyo bayan bukatar al’umma jihar ta Adamawa tare da gwamnatin jihar wanda hakan zai taimaka wajen horas da Likitoci har ma da inganta kiwon lafiya a fadin Jihar baki daya.

Ko a kwanan nan ma shugaban kasa Buhari ya amince da samar da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya a karamar hukumar Hong dake jihar ta Adamawa.

Ɗaga darajar cibiyar kiwon lafiya zuwa asibitin koyarwa zai kuma ɗaga mukamin Daraktan cibiyar wato Farfesa Auwal Abubakar da Mataimakin shugaban Jami ar Modibbo Adama Farfesa Liman Tukur da dai sauransu.

Murayar yanci da ta tattauna da wasu mazauna jahar Adamawa sun baiyanan farin cikinsu dagane da haka wanda acewarsu daman abunda suke jira kenan.

Labarai Makamanta