Da Dumi-Dumi: An Cimma Matsaya Tsakanin PDP Da Gidajen Yada Labarai Na Arewa

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, bayan shiga tsakani da wasu jiga-jigan PDP suka yi, an samu daidaito tsakanin jam’iyar PDP da kungiyar gidajen yaɗa labarai na Arewa, kan daukar rahotannin babban taron da jam’iyyar za ta yi.

Manyan kusoshin jam’iyyar wadanda suka haɗa da Alhaji Adamu Maina Waziri da Alhaji Kabiru Tanimu Turaki da sauran kusoshin jam’iyyar sune suka shiga tsakani wajen shawo kan rikicin.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da ta samu sanya hannun Shugaban Ƙungiyar Alhaji Abdullahi Yelwa Ajiyan Yawuri kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

“Muna sanar da dukkanin ‘ya’yan Ƙungiyar mu cewar mun samu daidaito tsakanin mu da PDP, bisa ga haka a yanzu mun janye wancan mataki da muka dauka.

Muna kira ga ‘ya’yan Ƙungiyar tamu da cewar a halin yanzu mun samu fahimtar juna, suna iya zuwa daukar rahotanni a wajen taron, sannan muna fatan za’a yi taro lafiya a gama lafiya.

Labarai Makamanta