Da Dumi-Dumi: An Bindige Kwamishina A Jihar Katsina

Rahoton dake shigo mana yanzu daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi wa kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir kisar glla.

An ruwaito cewa an bindige shi ne a gidansa da ke Fatima Shema Estate da ke birnin Katsina da yammacin nan.

Wata majiya wacce ta tabbatar da lamarin ta ce: “An bindige marigayi Nasir ne bayan sallar La’asar a gidansa da ke nan Fatima Shema Estate.”

Marigayi Dr Rabe Nasir mashawarci ne na musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari kan Kimiyya da Fasaha kafin a nada shi Kwamishina.

An haife shi ne a garin Mani da ke karamar hukumar Mani ta jihar Katsina.

Labarai Makamanta