Da Dumi-Dumi: An Amince INEC Ta Aike Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo

Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, yanzu majalisar dattawan Najeriya ta amince hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta yi amfani da na’ura domin aika sakamakon zaɓe.

Majalisar ta sauya ra’ayinta na farko inda ta ƙi amincewa da matakin game da tura sakamakon zaɓe daga muzaɓu ta hanyar intanet.

A zaman da ta yi na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce INEC za ta iya amfani da na’ura ta aika sakamakon zaɓe a lokacin da ya dace idan har hukumar kula da harakokin sadarwa ta Najeriya NCC ta amince.

Majalisar ta kuma kaɗa kuri’ar amincewa da tsarin gudanar da zaɓen fidda ƴan takara na jam’iyyu ta hanyar zaɓe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.

Labarai Makamanta