Da Dumi-Dumi: Alkalin Alkalai Ya Yi Murabus

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban Mai Shari’a na ƙasa, Justice Tanko Muhammad, ya yi murabus daga kujerarsa biyo bayan rikicin da ya barke tsakaninsa da sauran alkalan kotun kolin Najeriya.

Mai Shari’a Tanko Mohammad ya yi murabus ranar Lahadi kuma yace ya ajiye aikinsa ne sakamakon rashin lafiya.

Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana shirin nada Justice Olukayode Ariwoola, matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa za’a sanar da murabus dinsa nan ba da dadewa ba.

Labarai Makamanta