Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Katsina na bayyana cewar, Allah ya yi wa tsohon Ministan noma Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa a birnin Landan na kasar Ingila bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Majiyar mu ta shaida mana cewa Alhaji Abba Sayyadi ya rasu a wata asibiti dake a birnin Landan bayan ya ziyarci asibitin domin a duba lafiyarshi.
Abba Sayyadi Ruma wanda aka haifa a ranar 13 ga Watan Maris shekarar 1962 ya rike mukamin sakataren Gwamnatin jihar Katsina daga bisani ya zama Ministan Noma da kula da ruwan Nijeriya a lokacin Marigayi Ummaru Musa Yar’adua.
Marigayin shine wanda ya assasa Makarantar Koyon kiwon lafiya dake a Batsari da Katsina watau Cherish College of Health Sciences.
Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta mishi Allahumma Amin.