Da Ɗumi-Ɗumi: Rikici Ya Ɓarke A Majalisa

Rikici ya barke yanzu haka a daki na 028, inda aka shirya taron tattaunawa da jama’a kan dokar kamfanin man fetur PIB tsakanin wasu suka halarci zaman taron a zauren Majalisar dokokin tarayya.

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa har yanzu ba’a gane wadanda suka tada rikicin ba amma ana kyautata zaton wasu ‘yan jihohin yankin Neja Delta ne.

Rikicin ya barke da tsakiyar ranar ne lokacin da shugaban kwamitin, Hanarabul Mohammed Munguno, yayi kira ga ‘yan jihohin Neja Deltan su gabatar da jawabinsu.

Kawo yanzu, ‘yan majalisa da sauran wadanda ke hallare a wajen sun gudu daga dakin.

Ana samun fargaba matuƙa a duk lokacin da aka samu ɓarkewar rikici a zauren Majalisar dokoki, a mafiyawancin lokuta rikicin na faruwa ne tsakanin ‘yan Majalisar da junansu.

Sai dai ana ganin wannan rikicin ya sauya salo domin rikici ne da ya faru tsakanin wasu baƙi da suka halarci zaman majalisar.

Har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto dai ba a tantance ainihin gaskiyar abin da ya haifar da rikicin ba.

Karin bayani na nan tafe…

Labarai Makamanta

Leave a Reply