Da Ɗumi-Ɗumi: Fulani ‘Yan Bindiga Sun Karkashe Mutane Ba Adadi A Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar daruruwan jama’ar wasu ƙauyuka akalla biyar a yankin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar Zamfara na ci gaba da tserewa daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan Bindigar Fulani dake addabar yankin.

Shaidun gani da ido sun ce an kashe mutane sama da Talatin, da sace dabbobi da kayan abinci a lokacin waɗannan hare-hare.

Jihar Zamfara dai na cigaba da fuskantar kisan kare dangi daga hannun ‘yan Bindigar Fulani shekaru da dama, lamarin da ya kai ga tunbuke rawunnan wasu sarakunan gargajiya da ake Zargi da cin amana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply