Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Boko Haram Sun Dira Jihar Bauchi – Gwamnati

Gwamnatin Jihar Bauchi tace wadansu da ake Zargin ‘yan ta’adda ne na Kungiyar Boko Haram sun bullo a kananan hukumomi hudu na Jihar a sakamakon bullarsu a harin da suka kai a Gaidam ta Jihar Yobe, wacce take makubtaka da Jihar Bauchi

Hakan ya fito ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabiu Baba, bayan wani zama na gaggawa da gwamnatin tayi da shugabanin Jami’an tsaro a dukkan fadin jihar.

Sakataren ya kara da cewa rahotanni na nuni da cewa kana nan hukumomin da abun ya shafa, sun hada da Gamawa, Zaki, Dambam da Darazo û cikin Jihar Yobe tare da Barnata kayan sadarwa mallakar MTN a Karamar hukumar Gamawa.

Hakan nan Sabiu Baba yace a dalilin haka yasa Jami’an tsaro ala’tilas za a tura masu, Karin karfin tare da Jami’an tsaro na yan’banga da da sauransu a yankin msammannkan iyakar Jihar Yobe da Bauchi.

Shima kwamishinan Yan’Sanda na Jihar Sylvester Abiyodun Alabi yace Jami’an su sun kasance cikin Shirin ko ta kwana tun samun labarin bullar tasu, da boda haka za a tsaurara matakan tsaro da zagaya was lungu lungu, ba tare da wani bata lokaci ba,

Kana yace a cikin mutanen da ake Zargin bata kayan sadarwan kuwa yace Jami’an tsaro sun chafke mutum hudu da suke da alaka aukuwar hakan a yankin na karamar hukumar Gamawa.

Biyodun Alabi, ya kara kiran mutane a yankin da su kwantar da hankalinsu Kuma susa Idanu sosai duk inda suka ji wani abu to suyi saurin sanar da Jami’an tsaro dake kusa da su, don a dakile su, a cewarsu sai kowa ya bada tasa gudummuwar sannan za aci nasarar yakan Yan ta’adda a ko ina.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta