Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako ‘Yan Makarantar Jangeɓe

Labarin da ke shigo mana yanzu daga jihar Zamfara na bayyana cewar ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da ‘yan matan makarantar Sakandaren kwana ta Jangeɓe sun samu ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga.

A halin yanzu suna fadar mai martaba Sarkin Zamfaran Anka suna jirar motar da zai kai su Gusau babban birnin jihar.

Ɗaliban waɗanda suka haura 300 an sace su ne da dare lokacin da suke sharar barci a ɗakunan kwanan Dalibai na Makarantar, inda aka kurma kungurmin daji da su.

Kwana ɗaya da sace su wasu daga cikin ‘yan matan sun samu nasarar kubuta daga hannun ‘yan Bindigar, inda suka labarta halin tashin hankali da firgici da suka shiga a hannun ‘yan Bindigar.

An ruwaito gwamnan na jihar Zamfara Bello Matawalle ya samu ganawa da wasu manyan Kwamandojin ‘yan bindiga dake jihar domin tattauna yadda za’a sako ‘yan matan.

Da yawa daga cikin iyayen daliban da aka zanta dasu sun nuna tsoro da fargabar kada wani abu mummuna ya faru da ‘ya’yan nasu a hannun Bindigar, kamar fyade da kamuwa da cututtuka.

Labarai Makamanta