Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Sake Sace Ɗalibai A Kaduna

‘Yan Bindiga sun shiga makarantar Firaimaren UBE LEA dake Kauyen Rima, na Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka sace dalibai da malamai.

Mazauna garin sun bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 9 na safe yayin da daliban ke tururuwar zuwa makaranta ranar Litinin.

Abdulsalam Adam ya bayyana cewa ‘yan Bindigar sun je akan Mashina 12. Yace sun samu Rahoton cewa an sace malamai 3 da wasu dalibai amma suna kokarin tantance lamarin amma duk da haka ‘yan Bijilante sun bi bayan maharan.

Wani mahaifi ya bayyana cewa ya ga yaronsa akan mashin din ‘yan Bindigar suka tserewa dashi, hakanan shima wani mazaunin garin ya bayyana cewa akwai ‘yan uwansa 2 wanda na daga cikin malaman da aka sace.

Labarai Makamanta