Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba Da Fasinjoji A Neja

A kalla fasinjoji 50 ne yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Talata a kan hanyar Tegina zuwa Minna a karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, yan bindigan sun tare titi a garin Kundu da ke kusa da garin Zungeru suka kama motoccin fasinjoji uku har da direbobin motoccin.

Sun tisa keyar fasinjojin motoccin uku zuwa cikin daji yayin da suka bar motoccin a kan titi.

A wani lamari mai kama da wannan, yan bindiga sun sace mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba daga kauyen Gidigori da ke karamar hukumar Rafi, sun kona motocci biyar sun kuma sace kayayyaki.

Da ya ke tabbatar da wannan, wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a boye sunansa ya ce har yanzu ba a ji komai daga yan bindigan ba ballantana jami’an tsaro su san wadanda aka sace.

Kazalika, an halaka mutum daya an kuma yi garkuwa da wasu da dama yayin da yan bindiga suka afka garin Manta da ke karamar hukumar Shiroro a yammacin ranar Litinin.

Yan bindigan sun sace kayan abinci daga gidajen mutane da wasu kayayyakin.

An yi kokrin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun amma bai daga wayarsa ba.

Labarai Makamanta