Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Ƙwato Garin Marte

Rundunar Sojojin Najeriya ta sami nasarar kwato garin Marte dake jihar Borno daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Sojojin sun kuma sami nasarar hallaka mayakan ISWAP da na Boko Haram da dama yayin artabun tare da lalata makamansu masu dimbin yawa a yankin.

Wata majiya daga cikin sojojin ta tabbatarwa da kafar PRNigeria cewa dakarun sojojin sun kuma sami nasarar kwance bama-bamai da sauran abubuwan fashewa da dama kafin su kai ga kwace garin.

“Mun kwace garin Marte tun wurin misalin karfe 3:00 na rana kuma yanzu haka mu ke iko da garin. Mun kudiri aniyar ba za mu ba kasarmu da Sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro kunya ba,” inji majiyar.

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka tabbatar da cewa ’yan tada kayar bayan sun kwace iko da garin tare da kafa tutarsu a cikinsa na tsawon kwanaki.

Labarai Makamanta