Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin Saman Soji Yayi Hatsari A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na cewa wani jirgin sama na sojoji ya yi hatsari kusa da filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Majiyar mu ta bayyana cewa dukkanin fasinjoji da matukan jirgin sun mutu a hadarin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, a shafukansa na intanet, Ministan Sufurin Saman Nijeriya Sanata Hadi Sirika, ya ce jirgin kirar King Air mai lamba 350 ya fado ne a kan titin jirgin saman Abuja yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Minna, saboda matsala da injinsa ya samu.

Daga karshe yayi kira ga ƴan Nijeriya su kwantar da hankalinsu kan faruwar lamarin, Ministan ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Labarai Makamanta