Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Dakarun Soji

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Manjo Janar Yahaya Faruq a matsayin sabon Shugaban Dakarun Sojin Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Birgidiya Janar Onyema Nwacukwu ya fitar a yau Alhamis.

Kafin naɗin nashi Manjo Janar Yahaya shine babban Kwamandan rundunar soji dake yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso gabashin Najeriya mai suna Operation Haɗin Kai.

Nadin nashi na zuwa ne ‘yan kwanaki kaɗan da rasuwar tsohon shugaban Dakarun Sojin Janar Ibrahim Attahiru da wasu Soji goma a wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya afku a jihar Kaduna.

Labarai Makamanta