Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari Ya Dawo Najeriya Daga Landan

Rahotanni daga fadar Shugaban Kasa Abuja, na bayyana cewar Shugaban ya dawo gida Najeriya da yammacin wannan rana ta Alhamis bayan shafe makwanni Biyu da ya yi a Birnin Landan na ƙasar Ingila domin duba lafiyar shi.

Mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

Shugaba Buhari ya tafi birnin Londan da ke kasar Birtaniya ne ranar 30 ga watan Maris domin a duba lafiyarsa.

Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa, “don haka ba sabon abu ba ne,” kamar yadda Garba Shehu ya fada gabanin tafiyar shugaban.

Labarai Makamanta