Da Ɗumi-Ɗumi: Ba A Ga Jinjirin Wata A Saudiyya Ba

Rahotanni daga kasar Saudiyya na bayyana cewar masu aikin duban jinjirin wata basu samu ganin jinjirin watan Shawwal na ƙaramar Sallah ba.

Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga watan Shawwal a yau ba don haka Ƙaramar Sallah za ta kama ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021.

Dama tawagar da ke duban watan ta taru don duban jaririn watan na Shawwal.

An sanar da cewa rashin ganin watan ya shafi Saudiyya ne da duka ƙasashen da ke bin ranakunta.

A ɓangaren kasar Najeriya kuwa tuni fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta bada umarni duba jinjirin watan a yau, idan an yi nasarar gani gobe Laraba zata kasance ranar Sallah, idan ba a gani ba za’a cike Ramadan zuwa kwana 30 Alhamsi sai ayi salla.

Labarai Makamanta