Da Ɗumi-Ɗumi: An Yi Wa Buhari Allurar Rigakafin CORONA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin korona a ranar Asabar.

Likitan shugaban ne Dr Shu’aibu Rafindadi ya yi wa shugaban allurar misalin ƙarfe 11:53 a fadarsa a Abuja.

An kuma yi wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo allurar bayan yi wa shugaba Buhari.

An kuma gabatar da katin shaidar karɓar allurar ga shugaban da kuma mataimakinsa.

A jawabinsa bayan karɓar allurar, shugaba Buhari ya yi kira ga ƴn Najeriya su fito domin a yi masu allurar.

A ranar Juma’a ne Najeriya ta ƙaddamar da allurar rigakafin korona a ƙasar inda aka fara yi wa likitoci kafin shugabanni da kuma sauran ƴan ƙasa.

Allurar riga-kafin Oxford ta AstraZeneca Najeriya za ta karɓa a ranar Talatar makon da ya gabata.

Najeriya za ta kasance kasa ta uku a yankin Afrika Ta Yamma da suka ci moriya tallafin alluran riga-kafin karkashin shirin COVAX, baya ga Ghana da Cote D’Ivoire.

Labarai Makamanta