Da Ɗumi-Ɗumi: An Yi Garkuwa Da Ɗalibai Da Malamai A Jihar Neja

A daren ranar Talata ne da misalin karfe 2 na dare, wasu ‘yan bindiga suka shiga makarantar kwana ta Kagara dake jihar Neja, inda suka garkuwa da wasu dalibai da malaman makarantar.

Wani mazaunin rukunin gidajen malaman makarantar, ya shaida wa Aminiya yadda ‘yan bindigar suka tattara daliban da malaman, sannan suka yi awon gaba da su.

An gano yadda ‘yan bindigar sanye da kayan sojoji suka sulale da wanda suka sace din, ba tare da samun agaji daga jami’an tsaron jihar ba.

Ya zuwa yanzu kakakin ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, bai daga waya ba, bare a ji ta bakinsa game da faruwar lamarin.

Labarai Makamanta