Da Ɗumi-Ɗumi: Allurar Rigakafin CORONA Ta Iso Najeriya

Allurar rigakafin CORONA na Oxford-AstraZeneca da NAFDAC ta amince dasu sun iso kasar Najeriya da tsakar ranar Talatar nan a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta wani kamfanin jirgin sama na Emirates.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar na fadar shugaban kasa (PTF) kan COVID-19, Boss Mustapha, ya fada a ranar Asabar cewa Najeriya za ta karbi kaso na farko na kimanin allurai miliyan 4 na COVID-19.

A filin da aka karbi kayan rigakafin akwai manyan jami’an gwamnati da suka hada da Shugaban PTF, Boss Mustapha; da Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed; da Darakta-Janar na Cibiyar hana yaduwar cututtuka (NCDC) Chikwe Ihekweazu.

“An ce mana mu bude asusu da Afreximbank a karkashin Tarayyar Afirka; Mun riga mun yi hakan tuni saboda za mu biya kudin wani bangare na allurar rigakafin.

Alurar rigakafin ta COVAX kyauta ce, ba za mu karbi ko kwabo ba, an samar da ita ne ta hanyar gudunmawa,” in ji Mistan lafiya.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakinsa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha da sauran fitattun ‘yan Najeriya za su kasance cikin sahun farko na ‘yan Najeriya da zasu yi allurar rigakafin COVID-19 ta gidan talabijin kai tsaye.

Ana sa ran za su fara allurar ta farko a ranar Asabar, 6 ga Maris. Babban Darakta/Shugaba, na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaib, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi na Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan COVID-19.

Labarai Makamanta