Da Ɗumi-Ɗumi: Aisha Buhari Ta Dawo Daga Tafiyar Wata Shida

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan watanni shida da ta shafe a birnin Dubai na kasar haddadiyar daular Larabawa.

Mun samu labari daga majiya mai karfi cewa Aisha tana fadar shugaban kasa da ranan nan cikin walwala da koshin lafiya.

Uwargidar shugaban kasan ta tafi Dubai ne tun bayan auren diyarta, Hana, a Satumban shekarar 2021 da ta gabata.

‘Yan Najeriya dai sun yi ta maganganu akan tafiyar da Uwargidan Shugaban ta yi na tsawon lokaci babu amo ba labari.

Biyo bayan yawaitar surutan ne daga bisani ofishin Uwargidan Shugaban ya fitar da sanarwar cewa Aisha Buhari ta ziyarci birnin Dubai ne domin duba lafiyar ta.

Sai dai masu fashin baƙin al’amura na ganin cewa fakuwar Uwargidan Shugaban kasar bai rasa nasaba da rashin gamsuwa da salon yadda al’amura ke gudana a ƙasar ne, ƙarkashin jagorancin mijinta mai girma Shugaban kasa Buhari.

An samu labarin cewa ta dawo kasar da daren ranar Laraba.

Labarai Makamanta