Cutar Lassa Ta Zama Annoba A Najeriya – Masana

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Masana na ci gaba da nuna damuwa kan rahoton da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta fitar, wanda ta ce mutum 96 sun kamu da cutar zazzabin Lassa cikin kananan hukumomi 27 a jihohin kasar.

Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, kwarraren likita ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sahida wa BBC cewa adadin ka iya wuce haka idan aka fadada bincike.

Likitan ya ce,”Akwai tashin hankali saboda idan da har za a zurfafa bincike to ko shakka ba bu sai an samu ƙari a kan adadin, saboda cutar Lassa Fever ciwo ne wanda ko da mutum a wani lokacin ya kamu da ita kashi 90 cikin 100 ba sa nuna alama”.

Ya ce ko da za su nuna alamar ma to kadan ce, kaso 20 cikin 100 ne kawai ake samu na nuna lamar ciwon sosai.

Dr Kwaifa, ya ce cutar Lassa na da yanayin yaduwa kala biyu, wato akwai beran dake dauki da kwayar cutar kan yadata ga mutane idan ya yi mu’amala da wani abin rayuwa na mutum.

Hanya ta biyu kuma da ake kamuwa da cutar itace wanda ya ke dauke da ita kan yadawa wanda bashi da ita muddin suka yi mu’amala tare.

Kwararren likitan ya ce cutar Lassa fa na da alaka da gurbatar muhalli, saboda duk in da aka samu kazanta ko ta tara bola da makamancinsu to bera kan yi zirya a wajen.

Dr Kwaifa, ya ce bayan zazzabi mai zafi da cutar Lassa kan sawa mutum, ta kan kuma gurbata jini mutum ta yadda mutum zai ga yana zubda jini haka kawai.

“Haka kuma cutar na bata wasu bangarori na jikin dan adam kamar hanta da koda da kuma kwakwalwa” in ji likitan.

Ya ce, bayan haka kuma wasu mutane da suka kamu da cutar kan yi gudawa da amai abin da kan janyo ruwan jikin mutum ya yi kasa.

Labarai Makamanta