Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 65 sun kamu da korona a faɗin Najeriya a ranar Juma’a.
Alƙalumman sun nuna jihar Kaduna ce ta fi yawan waɗanda suka kamu a ranar Juma’a da mutum 20.
Sai jihar Gombe inda aka samu ƙarin mutum 10. A Abuja an samu mutum 9.
Ga jerin jihohin da aka samu ƙarin masu korona a Najeriya
Kaduna-20
Gombe-10
FCT-9
Rivers-9
Bauchi-6
Lagos-3
Delta-2
Edo-2
Kano-2
Oyo-2
jimillar mutum 212,511 yanzu korona ta shafa a Najeriya amma 204,184 sun warke.
Cutar kuma ta kashe jimillar mutum 2,902 a Najeriya
You must log in to post a comment.