Coronavirus: Gwamna Matawalle Ya Dakatar Da Kai Dalibai Kasar Sin

Gwamnatin jihar Zamfara ta soke tafiyar dalibai 20 da ta dauka nauyin karatunsu zuwa kasar China a karkashin tallafin gwamnatin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Bello Matawalle ya sama wa dalibai 200 na jihar gurbin karatu a makarantu daban-daban na fannin kimiyya da fasaha. An samu guraben karatun ne a kasar India, Sudan, Cyprus, China da sauransu.

Hukumar daukar nauyin karatun ta jihar Zamfara din ta tantance daliban da suka samu nasara. A cikinsu kuwa wasu na kasashe daban-daban sun fara tafiya karatunsu.

Sakamakon barkewar muguwar cutar coronavirus, daliban da aka yankewa tafiya kasar China an dakatar da tafiyarsu.

Mai bayar da shawara na musamman ga gwamna Matawalle a kan lamurran daukar dawainiyar karatu, Lukman Majidadi, wanda ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya wannan cigaban, ya ce an yi hakan ne don kariya ga rayukan matasan maza da mata.

“Don kariya ga daliban Najeriyan da kasar baki daya, mun yanke hukuncin soke tafiyar matasa 20 da suka samu guraben karatu a kasar China din. A halin yanzu muna kokarin samar musu da guraben karatu a wasu kasashen da ke lafiya.

Mun sanar da daliban da abin ya shafa tare da kiran su a kan kada su damu tunda gwamnan ya basu damar. Umarni ne kuma za a tura su makaranta,” Lukman ya tabbatar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa ana tsammanin daliban za su karanci fannin likitanci, na’ura mai kwakwalwa, zane da kimiyyar gine-gine da sauransu.

Related posts