CORONA: Zamu Mayar Da Yaki Da Cutar Hannun Gwamnoni – Buhari

Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa a kan yaki da cutar korona PTF, ya ce a yayin da zai ci gaba da hadin gwiwa tare da gwamnonin jihohi, ya kuma fara shirin sauya salon daukar mataki na gaba a kan annobar, Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamitin zai dage a kan mayar da akalar yaki da cutar korona a hannu gwamnoni, domin su ci gaba da cin gashin kansu wajen daukar matakai na dakile annobar.

Babban jami’i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa, Sani Aliyu, shi ne ya sanar da hakan yayin zaman karin haske tare da sauran ‘yan kwamitin a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Mista Aliyu ya ce kwamitin zai ci gaba da goyon bayan gwamnonin wajen daukan matakai da zartar da hukunci, tare da yi masu kyakkyawan tanadi na tsare-tsaren da mahukuntan lafiya suka gindaya.

Sai dai ya ce “amma ba za mu ci gaba da daukar wa jihohi matakai ba kai tsaye daga bangaren gwamnatin Tarayya.

Related posts