CORONA: Za Mu Cigaba Da Jigilar Almajirai Zuwa Jihohin Su Na Asali – Gwamnonin Arewa

Gwamnonin 19 na yankin jihohin Arewacin Najeriya sun ce sun shirya cigaba da maida Almajirai zuwa garuruwansu na asali. Rahoton ya bayyana jagoran kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, Gwamnan jihar Filato Solomon Lalung ta bakin Sakataren gwamnatin jihar Filato, Danladi Atu ya yi wannan bayani a wata hira da aka yi da shi.

Atu ya ce: “Ba mu kammala dauke Almajirai a yankin ba. Gwamnonin Arewa za su zauna kwanan nan, su sa ranar da za a cigaba da maida Almajiran inda su ke fito.

Danladi Atu ya kara da cewa “Amma wannan zai kasance kusan zuwa bayan Sallah.”
A cewar jagoran na kungiyar Gwamnonin, akalla Almajirai 11, 000 aka maida gidajen da aka haife su a jihohin Arewa a lokacin da annobar COVID-19 ta soma aukuwa.

Idan ba ku manta ba, annobar COVID-19 ta fara kamari ne a Najeriya a watan Mayu. Fiye da watanni biyu kenan ana fama da Coronavirus a kasar nan.

Mista Danladi Atu ya ce a baya gwamnonin yankin sun rika maida almjarai, amma yanzu an dakatar da wannan lamari ne domin bin umarnin shugaban kasa.

Kwanakin baya sakataren gwamnatn tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya haramtawa gwamnonin Arewa yawo da almajrai daga wuri zuwa wuri. Yanzu da kwamitin ya dakatar da wannan doka, za a koma aikin da aka faro na maida Almajran zuwa kauyuka da garuruwan da iyayensu su ke inji Atu.

Labarai Makamanta