CORONA Ta Kama Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin fitattun mutane a Najeriya waɗanda cutar nan ta sarƙewar numfashi Coronavirus/COVID-19 ta kamashi a kwanakin baya.

Chief Olusegun Obasanjo yace amma bayan awanni 72 da aka sake masa gwaji sai aka tabbatar mishi da cewa ya warke tatas daga cutar, kuma zai cigaba da gudanar da harkokin shi ba tare da tarnaki ba.

Obasanjo ya bayyana hakane a wajan bikin zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekaru 84 da haihuwa.

Obasanjo yace amma cutar bata nuna wata Alama ba a jikinsa, kuma bayan nan an masa gwaji har sau 3 kuma duk sun nuna cewa bashi da cutar.

Cutar CORONA cuta ce dake saurin yaɗuwa cikin jama’a, amma idan aka bi matakan kariya abubuwa suka zo da sauki.

Daga cikin dubban mutane da CORONA ta kama a Najeriya sama da rabi sun warke daga cutar tare da cigaba da gudanar da harkokin su.

A cikin wannan makon da muke ciki ne Rigakafin Allurar CORONA ta shigo Najeriya, kuma tuni Gwamnatin kasar ta yi kira ga jama’ar kasar su rungumi yin Allurar Rigakafi.

Labarai Makamanta