CORONA: Mutane Miliyan 25 Sun Harbu A Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya kiyasta cewar mai yiwuwa yawan kasar da suka kamu cutar coronavirus ya kai miliyan 25, abinda ya sanya shugaban rokon da a dauke annobar da muhimmanci.

Rouhani ya bayyana haka ne a yau asabar, inda yace ma’aikatar lafiyar kasar ta Iran ce ta tattara alkalumman, bayan binciken da ta gudanar.

Shugaban ya kara da cewar, a wani kyasin na daban, kimanin karin Iraniyawa miliyan 30 zuwa 35 ne cikin hadarin kamuwa da cutar ta coronavirus, kusan kashi 50 na yawan al’ummar kasar ta Iran mai yawan mutane miliyan 81 jumilla.

A halin da ake ciki annobar at coronavirus ta fi yiwa Iran illa a yankin gabas ta tsakiya, bayan halaka mata mutane dubu 13 da 979, daga cikin sama da dubu 270 da suka kamu da cutar.

Labarai Makamanta