Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 499 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.40 na daren ranar Alhamis 9 ga Yulin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 499 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
Lagos-157
Edo-59
Ondo-56
Oyo-31
Akwa Ibom-22
Borno-21
Plateau-19
Kaduna-18
Katsina-18
Bayelsa-17
FCT-17
Delta-14
Kano-11
Rivers-10
Enugu-8
Ogun-6
Kwara-4
Imo-3
Nasarawa-2
Osun-2
Abia-1
Ekiti-1
Niger-1
Yobe-1
30748 ne jimmilan wadanda suka kamu
12546 aka sallama kawo yanzu
689 sun mutu
You must log in to post a comment.