Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:27 na daren ranar Jumaa 28 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Plateau-44
Lagos-27
Katsina-18
Edo-15
Abuja-14
Ondo-10
Oyo-9
Kwara-6
Abia-4
Nasarawa-4
Kano-3
Ekiti-2
Kaduna-2
Kebbi-1
Jimillar wadanda suka kamu – 53,477
Jimillar wadanda suka warke – 41,017
Jimillar wadanda cutar ta kashe – 1,011
You must log in to post a comment.