CORONA: Masu Biredi Sun Yi Barazanar Kara Farashi

Masu gidajen biredi na jihar Legas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga lamarinsu a kan yadda kayayyakin aikinsu ke tashi. Hakan zai iya shafar farashin biredin da karin kashi 60 a nan kusa.

Masu gidajen biredin sun koka a kan cewa kayayyakin sun tashi ne sakamakon annobar COVID-19 da ta zama ruwan dare, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

A wata takarda da shugabannin kungiyoyin na jihar Legas, Kwamared Taiwo Akintola da Kwamared Ibitoye Oladapo suka saka hannu, kungiyoyin sun nuna damuwarsu matuka a kan halin da suke ciki.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana, tashin farashin kayan na iya kashe kasuwancinsu domin suna matukar shan wahala wajen fitar da riba.

“Buhun fulawa da ke N9,000 kafin COVID-19 yanzu N13,000. Buhun sukari kuwa da ke N13,000 a da yanzu ya kai N24,000. “Bota a halin yanzu N12,000 ne a maimakon N7,500. Madara a da N29,000 take amma a yanzu N52,000,” kungiyar tace.

Sun kara da cewa farashin yis da sauran sinadaran da ake zubawa biredin duk ya yi tashin gwauron zabi.

Kungiyar ta yi bayanin cewa rashin daidaituwa a bangaren canji, farashin man fetur da sauran kayayyaki na daga cikin dalilan da suke kawo tashin farashin fulawa. Kungiyar ta yi kira ga masu kamfanonin fulawa da sauran kayayyakin hadin biredin da su sassauta farashin amma har yanzu shiru. “A saboda haka ne muke mika kokon barar mu ga gwamnatin tarayya da ta saka hannu a al’amarin don farashin kayayyaki su sauka kasa.

Related posts