CORONA: Kowa Ya Yi Sallar Idi A Gidanshi – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, sun umarci daukacin Musulmin Najeriya kowa ya gudanar da Sallar Idi a gida, gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Cikin wata sanarwar da JNI ta fitar ta hannun Babban Sakatare Khalid Aliyu, ya ce tunda an hana cunkoson jama’a cikin har da gwamutsuwar jama’a a wuraren ibada, ya kamata Musulmi su bi wannan umarni, domin kawar da wannan cuta ta Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta umarci a fara duban watan 1 Ga Shawwal a ranar Juma’a kafin Sallar Magriba da kuma bayan Magriba.

Cikin sanarwar da JNI ta fitar, ta ce kowa ya yi Sallar Idi a cikin gida tare da iyalin sa.

Related posts