CORONA: Gwamnatin Neja Ta Kara Wa’adin Zaman Gida

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar inda zaa cigaba da zaman Gida.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron mako-mako da yake yi da mambobin kwamitin yaki da cutar Coronavirus na jihar.

Sannan ya nuna damuwarsa da yadda mazauna jihar sa ke ta ke dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Yace Abin takaici ne yadda muka rufe iyakokinmu tsakaninmu da wasu jihohin amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba Masu babura suna yawan kaiwa da kawowa wanda hakan ke nuna karantsaye ga dokar gwamnatin.”

Gwamnan ya sanar da dokar hana aikin babura a jihar na makonni biyu yayin da duk sauran dokokin za su ci gaba da aiki na tsawon makonni biyun.

A karshe Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su kiyaye tsaftar kansu, zama nesa-nesa da juna, saka takunkumin fuska idan za a shiga jama’a da kuma gaggauta neman shawarar masana kiwon lafiya yayin da wata alamar cutar ta bayyana ya kuma nemi duk wadanda suka dawo daga tafiya su killace kansu.

Related posts