CORONA: An Kafa Dokar Hana Fita A Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a fadin jihar da niyyar dakile yaduwar cutar coronavirus.

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta sanar da cewa dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren yau Alhamis, har sai abin da hali ya yi.

Hadiza Balarabe ta ce dokar ta tilasta wa jama’a zama a gida, tare da haramta zuwa cibiyoyin kasuwanci da halartar wuraren ibada.

Dokar ta kuma haramta dukkan tarukan jama’a da bukukuwa.

Sai dai dokar ba ta shafi masu ayyuka na musamman da suka hada da ma’aikatan lafiya da ‘yan kwana-kwana da jami’an tsaro da masu jigilar mai zuwa gidajen mai da sauransu.

Kazalika dokar ta yi rangwame ga matafiya da za su bi ta jihar Kaduna zuwa wasu jihohi, cewa za su iya bi ta hanyoyin wajen gari (Western bye-pass).

Related posts