Cire Tallafin Mai Zai Jefa ‘Yan Najeriya A Wagegen Rami Gaba Dubu – Mahadi

An bayyana cewar babu shakka ko kokwanto cire tallafin fetur da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta yi zai jefa ‘yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tsadar rayuwa inda komai a kasar zai yi tashin gwauron zabo fiye da yadda ake zato.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mashahurin ɗan kasuwar nan mazaunin Garin Kaduna Dr Mahadi Shehu lokacin da yake tsokaci akan cire tallafin fetur a wata ganawa da yayi da manema labarai a Kaduna.

Dr Mahadi ya kara da cewar tun farko Najeriya ba ta mori shugabanni ba ne masu kishi wadanda ya kamata su yi amfani da arzikin ƙasa yadda ya kamata wajen inganta rayuwar al’umma, sai ya zamana shugabanni ne waɗanda suka mayar da hankali wajen watanda da dukiyar ƙasa.

“Allah Ta’ala na ƙaunar kasar Najeriya ya zamana cewa dukkanin arzikin da wata kasa za ta yi tutiya dashi Allah ya bar kasar, sannan Allah ya sanya wa talakawan ƙasar hakuri fiye da kowace ƙasa a duniya inda matsalar take shugabannin kasar suka ci amanar ‘yan kasar maimakon talakan ya kasar ya zama sahun gaba wajen more jin daɗin rayuwa, sai ya zama na gaba wajen shan wahala a duniya.

Babban ɗan Kasuwar ya bayyana cewar a wannan tallafi da gwamnati ta cire zai sanya farashin mai ya yi tsada kamar yadda ake gani yanzu wanda sakamakon hakan zai haifar da tsadar rayuwa a kasar, Motocin haya da masu zaman kansu za su gagari kundila wajen hawa, kayayyakin masarufi da bangaren kuɗaɗen makaranta da Asibitoci da kudaden haya komai zai tashi lamarin zai zama sai “Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!!!

Daga karshe babban ɗan Kasuwar ya bayyana cewar kasashen Duniya waɗanda suka cigaba kamar kasar Saudiyya ko nawa gwamnati ta kara a farashin mai ba zai cutar da jama’ar kasar ba saboda dukkanin abin da ɗan Adam zai buƙata na jin daɗi a rayuwa Gwamnati ta samar abin da ya danganci tsaro, ilimi da lafiya, saɓanin Najeriya wadda a kullum ake yanayi na gara jiya da yau.

Labarai Makamanta