Cire Tallafin Mai Zai Jefa Talaka Cikin Kunci Da Wahala – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman Wanda akafi sani da Mr LA ya bayyana ra’ayinsa Dangane da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya take yunkurin aiwatarwa.

Tun a farko dai gwamnatin tarayya na biyan kudin tallafin man fetur ne domin saukake wa ‘yan najeriya farashin man fetur. Amma ko a wannan mako bankin duniya da masana tattalin arzikin Kasa sun shawarci kasar data cire tallafin man fetur domin a cewarsu baya anfanar ‘yan kasa Sai wasu tsiraru mutane da masu madafun iko.

Gwamnatin tarayya tace zata maye gurbin kudin tallafin man fetur da biyan naira Dubu 5 ga yan najeriya mutum miliyan 40.

A nashi martanin shahararren Dan siyasa Kuma Dan kasuwa honorabul Mr LA yace Babu abinda hakan zai haifar sai Kara kuntatawa talaka domin duk hauhawan farashin da za a samu na sufuri sakamakon karin kudin Mai dole zai shafi kayayyakin masarufi. Gwamnoni da sauran masu goyon bayan wannan cire tallafin su kadai zai anfana.

Saboda dole kudaden da gwamnatin tarayya take Basu zai karu ta yadda zasu kara azurta kansu da abokansu, a lokacin da dole talaka saiya siya abinda yake siya Dubu daya idan aka Kara kudin Mai dole saiya siyeshi kusan Dubu daya da da dari biyar zuwa Dubu biyu. Kuma su ko kadan bazai shafe su ba domin suna Kan madafun iko.

Mr LA yace inda gwamnatin buhari nada kunya Bai kamata ace a Mulkin shugaba buhari zai cire tallafin man fetur ba domin kowa ya ganshi a sahun gaba wurin zanga zangar yakar cire tallafin man fetur a shekarar 2012 a Mulkin shugaba Goodluck Jonathan.

A karshe Mr LA yace gwamnatin tarayya Bata da mashawarta masana tattalin arziki domin inda akwai masu hikima da hangen nesa, Babu wani dalilin cire tallafin man fetur a halin da kasar ke ciki na matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

Idan ka zauna kayi lissafi Babu wani dalilin cire tallafin man fetur domin ko a yanxu gwamnatin buhari tana biyan naira triliyan 1.8

Idan kayi lissafi zaka ga idan aka ba mutane miliyan 40 naira Dubu 5 kowannensu za a dinga kashe naira biliyan 200 duk wata. A shekara daya kachal gwamnatin buhari zata kashe biliyan 200 sau 12 zai Zama an kashe triliyan 2.4 kenan.
Meye anfanin Kara kashe kudin najeriya a kan abinda Babu abinda zai haifar sai tsadar rayuwa ga talakawan Kasa? Inji Mr LA

Labarai Makamanta