Cire Tallafin Fetur: Dan Kasuwa Ya Nuna Damuwarsa

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Wani Dan Kasuwa Dake Babban Birnin Tarayya Abuja Mai Abubakar Ibrahim Ya Bayyana Matakin da Gwamnatin Tarayya ta Dauka na Cire Tallafin Mai Babu Abinda zai Karawa Talakan Kasarnan Face Ukuba Fiye da Wacce Yake Ciki .

Abubakar Ibrahim Yace Maimakon cire Wannan Tallafi Kamata Yayi Gwamnati ta Maida Hankalinta akan abinda zai Taimaki Rayuwar Talaka kamar Samar da Wutar Lantarki Tsayayya da Kuma Inganta Kiwon Lafiya yadda Talaka zai rika Zuwa Asibiti Kyauta da kuma Samar da Ingantaccen Ilimi ta Hanyar gyara Tsarin Makarantu da Karantarwa da kuma Kyautatawa Malaman.

Ya Kara da cewa halin Zullumin da Al’ummar kasarnan ke ciki a yanzun Musamman na tabarbarewar Harkar tsaro bai kamata ace an cire Tallafi ba, Domin Tun Yanzun Wasu Masu Gidajen Mai a Sassa Daban Daban na kasarnan sun wasa wukarsu akan Talakawa masu amfani da Man Feturdin.

Daga Karshe ya Roki Wadanda Abin ya Shafa Su Duba hanyar da Talaka Zai Samu Sauki, kana yayi kira ga Yan Nijetiya Su Kara Rokon Allah Ya kawo Sauki a dukkan Halin da kasarnan Ke Ciki.

Labarai Makamanta