Cire Tallafin Fetur: Babu Gwamnan Da Zai Yi Tawaye – El Rufa’i

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai, ya ce a shirye gwamnatocin jihohi suke su goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur baki daya.

Jaridar Vanguard ta ambato gwamnan yana bayyana hakan ranar Talata a wajen gabatar da sabbin bayanai na Bankin Duniya reshen Najeriya da aka gudanar a Abuja.

El-Rufai, wanda ya yi bayani ta intanet, ya ce idan ba a cire tallafin man baki daya ba, watakila jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashi a shekarar 2022 ba.

A cewarsa, an dade da cire tallafin kalanzir, wanda shi ne ya fi yi wa talakawa amfani ba tare da wata matsala ba, yayin da aka cire tallafi a kan gas wanda manyan motoci suka fi yin amfani da shi .

“Ce-ce-ku-cen da ake yi kan fetur abu ne da a matsayinmu na kasa dole mu tattauna a kansa sanna mu amince kan yadda za a kawo karshensa,” in ji gwamna na jihar Kaduna.

Labarai Makamanta