Cinye Filin Jami’a: ASUU Ta Yi Barazanar Maka Ganduje Kotu

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta yi barazanar maka Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a kotu, matuƙar bai dawowa da jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano, gine-ginen ta da ya karɓe da kuma filayenta da ya sayar ba.

ASUU, reshen Jami’ar Yusuf Maitama Sule, wacce jami’ar gwamnati ce, ta yi wannan barazana ne a wata sanarwa da shugabanta, Dakta Abdulrazaƙ Ibrahim ya sanyawa hannu, ya kuma rabawa manema labarai a ranar Asabar.

A sanarwar, ASUU ta zargi Ganduje da karɓe wasu muhimman gine-gine da su ka haɗa da Sashin Koyar da Likitanci da ke Kwanar Dawaki da kuma Cibiyar Koyar da Harkokin Kasuwanci da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa.

Bugu-da-ƙari, ƙungiyar ta zargi Ganduje da sayarwa da rarraba filaye mallakarta a Babban Sashen jami’ar da ke titin Muhammadu Buhari.

ASUU ta yi ƙorafin cewa, shi wannan Sashen Koyar da Likitancin da Ganduje ya karɓe, ya tilastawa ma’aikata da ɗaliban wajen tashi da kuma yin karere a wasu ɓangarori na jami’ar.

Ta kuma yi kukan cewa ɗaliban sashen na wahala wajen jigilar zuwa ɗaukar darasi tsakanin ɓangarorin jami’ar.

Haka-zalika, ƙungiyar ta koka da cewa karɓe Sashen Koyar da Harkokin Kasuwanci da gwamnatin Ganduje ta yi a Dawakin Tofa ya rushe Karatun Shiga Jami’a, IJMB da kuma koyar da harkokin kasuwanci a jami’ar.

ASUU ta ƙara kokawa da cewa irin wannan karɓe gine-ginen da kuma sayar da filayen jami’ar zai kawo mata naƙasu a wajen ci gabanta.

Sabo da haka, ASUU ɗin ta yi kira ga Ganduje da ya tsaya da saide-saiden filaye da karɓe-karɓen gine-gine a jami’ar.

Sannan ta yi kira ga gwamnan da ya gaggauta dawo da waɗanda ya karɓe ya kuma sayar, in da ta ce, in ba haka ba, ba ta da wani zaɓi illa ta maka shi a gaban ƙuliya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply