Gwamnatin Ghana ta mayar da martani ga zarge-zargen da gwamnatin Najeriya ta yi mata na keta ƙa’idojin diflomasiya na kasa-da-kasa da kuma muzgunawa ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasarta.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta Ghana ta fitar ta hannun ministan watsa labaranta Kojo Nkrumah ranar Lahadi, gwamnatin ta Ghana ta musanta dukkan zarge-zargen kuma ta ce ta damu da kalaman da ministan harkokin watsa labaran Najeriya ya yi kan dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Game da zargin kwacewa ofishin jakadancin Najeriya wani gini da ke birnin Accra, Ministan na Ghana ya ce ba daidai bane kuma ofishin jakadancin ya karɓ ginin hannun wani ɗan ƙasa mai zaman kansa, Thomas D. Hardy a shekarar 1959.
A cewarsa, yarjejeiyar da suka sa wa hannu ta ƙare aiki tun shekara 46 da suka gabata ba tare da Najeriya ta sabunta yarjejeniyar ba.
Nkrumah ya kuma ƙaryata zargin da Najeriya ta yi na rushe wani gini mallakar ofishin jakadancin da ke lamba ta 19/21 layin Nyerere Street a birnin Accra. Ya ce ba gwamnatin Ghana ce ta rushe ginin ba amma kuma gwamnatin ta ɗauki nauyin sake gina ginin da aka rushe domin hana taɓarbarewar dangantaka tsakaninta da Najeriya.
Da yake jawabi kan batun tusa ƙeyar wasu ‘yan Najeriya kuwa, Nkrumah ya ce waɗanda aka tusa ƙyarsu mutum 700 ne kuma an same su ne da laifin aikata miyagun laifuka kamar damfara da karuwanci da fashi da makami.
Tun farko ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce ‘yan Najeriya 825 Ghana ta mayar Najeriya tsakanin 2017 zuwa 2019.
Gwamnatin ta Ghana ta kuma yi magana kan zargin rufe shagunan ‘yan Najeriya a shekarar 2019 zuwa 2020, ta ce bayan da gwamnati ta gano akwai rashin bin ƙa’idojin kasuwanci daga dukkan ‘yan ƙasa da baƙi, ta yi ƙoƙarin tattaunawa da su da basu shawarar cika ƙa’idojin amma suka yi burus.
A cewarsa, haka ne ya sa doka ta yi aikinta. Sai dai sanarwar ta ce ministan masana’antu ya sa baki aka buɗe shagunan da aka rufe tare da basu lokaci domin cika sharuɗan.
Sanarwar ta ce a halin yanzu, babu wani shagon ɗan Najeriya da yake rufe a Ghana.
Sanarwar ministan Ghanan na zuwa ne kwana biyu bayan wadda takwaransa na Najeriya ya fitar yana zargin Ghana da muzgunawa ‘yan Najeriya da ke can da kuma nuna wa kasar Najeriyar tsana a fili.
You must log in to post a comment.